Skip to main content

INA MA TSAYAR HAUSAWAN JOS A SIYASA?

Al’ummar Hausawa musamman wanda suke zaune a cikin birnin garin Jos ta arewa, sun kasance masu bada gudumawa wajen cigaban jahar Filato a fani daban daban kama daga kasuwanci, zamantakewa, hada har da siyasa, amma babban abun tamabaya anan shine ko shin su al’ummar ina suka dosa, ko muce ina tasu tsayar su a siyasar dubu biyu da ashirn da uku (2023). Amma bari muyi duba da irin gudumawar da suka bayar wajen kafuwar gwamnatin Lalong IRIN GUDUMAWAR DA SUKA BAYAR WAJEN KAFA GWAMNATIN LALONG A sheharar dubu biyu da goma sha biyar al'ummar Hausawan garin Jos suka bada gudumawa sosai wajen kafa gwamnati maici a karkashin Rt. Honorable Simon Lalong inda suka bashi kuri’a mafi tsoka wanda ku shi, Gwamnan naji shi ya sha fadin cewa badan kuri’ar suba da laile ba zai kawo gaci ba. inda kuma yayi alkwarin saka masu da romon demokaradiyya. Ko shin ya saka masu? Bari muyi duba da irin alkawarin da ya dauka masu kafin hauwar sa mulki.

1. GYARA BABBAR KASUWAR TERMINUS A yayin da yake neman kujerar gwamna a 2015 Simon Lalong yayi alkwarin cewa zai gyara ita wanna kasuwa, domin kasuwanci ya bunkasa tare da rage rashin aikin yi, amma tun bayan da ya hau kan karagar mulki ba wani abu zo a gani da za'a ace an sake ji mai inganci game da gyara kasuwar, sai dai a wani lokacin da ake daf da zaben 2019, Gwamna Lalong ya waiwaye ita wannan kasuwa inda ya fadawa al’ummar Jos ta arewa cewa yanzu an gama komai da wanda zasu gyara kasuwar har an ware Naira Biyon Daya wajen rusa kasuwar. Amma tunda aka rusa wani yanki na kasuwar har yanzu ba ko motar kasa daya da aka kawo, sai dai ma zargin gwamnatin Lalong da salwantar da karafen da aka cire a yayin rusa wani ban gare na kasuwar. Amma kuma acikin shekarar 2022 aka kara jin cewa wai Gwamnatin jahar filato tare da hadin gwiwar bankin muslunci wato Jaiz zata gyara kasuwar wanda har yazu ba a sake ji ko ina maganar ta kwana ba. Zamu iya cewa dai kawai gwamantin Lalong tayi kokari wajen yaudarar al’ummar Jos musamman hausawa wajen neman kuri’ar suba tare da ta cika masu wannan alkawarin ba. A hira da mukayi da wasu mazauna kasuwar sun nuna cewa tabbas da za’a gyara wannan kasuwar da ta kawo cigaba ma jahar Filato da ma kasa baki daya, amma sun danganta kin gyarawar da baya rasa nasaba da kabilanci duba da yarda cewa su hausawan sune mafi amfana da wannan kasuwa. 


 2. BUNKASA CIKIN BIRNIN JOS Wani daga cikin alkwarin da gwamnatin APC mai mulki tayi wa al’ummar Hausawan Jos shine bunkasa cikin garin da hanyoyi tare da kuma kara fadin garin, amma bisa dukkan alamu dai wannan alkawarin shima yana kokarin zama tarihi kamar yarda sauran yan siyasa suke ma jama’a. Domin zamu iya cewa banda titin Anguwan rogo wanda shima kasa da kilomita shida da ya dauki gwamnatin sama da shekara biyu kafin ta kammala ba wani abun azo a gani da za’ace ta aiwatar ma al’ummar Hausawan Jos. A lokacin da damuna take kara kusantuwa acikin garin Jos yana kasancewa mafi kazanta a duk sanda akayi ruwan sama, domin bayan ruwa ya sauka manyan titunan garin kan cika da shara da sauran datti dake barazana ga lafiyar yanki. Bayan nan wanda ya bar garin Jos shekara ashirn idan ya dawo zai iya kama hanyar zuwa gida domin kuwa yarda yabar garin hakan zai dawo ya same sa ba tare da wani alamun samun chanji ba, akan hanyiyoyi.

Comments

  1. Allah ya kyauta. Amma dai kam ya kamata alumma su lura wajen zaben shugabani

    ReplyDelete
  2. Maganar Mai magana ta farko Mai rubutu Yakoma baya lokachin da akeneman afara gyara Mai mutanen gari suke Chewa,har zanga zanga sukayi SUNA fadin basu yarda ba.

    ReplyDelete
  3. Ubangiji Allah ya kyauta, kuma yasa mu matasa mu gane yancinmu a koda wannane lokaci kuri’armu yancinmu

    ReplyDelete
  4. Wllhi especially government school, primary school , & secondary school, wllhi kullum yau I jiya, education system nothing nothing

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

Bridging Digital Divides: Empowering People with Special Needs and Uniting Communities Through Technology

By Abdullahi Abdulhafiz Aliyu In today’s fast-changing digital landscape, access to technology is no longer a luxury—it is a necessity. Yet, for millions of Nigerians, especially people with special needs, the digital world remains out of reach due to systemic barriers and a lack of inclusive learning opportunities. My work as a journalist and digital advocate has focused on breaking these barriers, ensuring that technology serves as a tool for empowerment rather than exclusion. Through my engagement with individuals with disabilities and as the host of Duniyar Fasaha (Fasaha World) on Unity FM, I have worked to bridge the digital divide by providing foundational digital education to marginalized groups. By introducing people with special needs to basic computer skills such as Microsoft Word, Excel, PowerPoint, and internet navigation, I have witnessed firsthand how technology can unlock new opportunities and transform lives. Digital Skills for Special Needs: A Path to Inclusion Inclu...

Tragedy in Bukuru: Trader Killed, Two Injured in JMDB Task Force Operation

A tragic incident occurred in Bukuru, Jos South LGA, on Monday, resulting in the death of a trader, Nasiru Abubakar, and injuring two others. The incident happened during an enforcement operation by the Jos Metropolitan Development Board (JMDB) task force. The Nigerian Police Logo According to reports, the task force was attempting to disperse a group of criminal elements when a warning shot was fired, unfortunately hitting the trader. The incident also resulted in the destruction of several vehicles, with over five cars set ablaze. The Commissioner of Police, Emmanuel Adesina, promptly visited the scene to assess the situation, and normalcy has been restored. The police command has issued a stern warning to individuals with criminal intentions, urging them to desist from their activities or flee the state. 

Reps Approve Tinubu’s Emergency Rule Request for Rivers State

 The House of Representatives has approved President Bola Ahmed Tinubu’s request to impose a state of emergency in Rivers State following heightened political tensions and security concerns. The decision, made during a plenary session on Wednesday, comes after weeks of instability in the oil-rich state, where political clashes and reports of pipeline vandalism have raised national security concerns. Why the Emergency Rule? The crisis in Rivers State stems from an ongoing power tussle between Governor Siminalayi Fubara and state lawmakers, a situation that has escalated into widespread unrest. Reports also indicate that increased incidents of oil theft and pipeline vandalism are affecting Nigeria’s economic stability. President Tinubu, in his emergency rule proclamation, suspended Governor Fubara and other elected officials, appointing retired Vice Admiral Ibokette Ibas as the military administrator to oversee the state’s affairs. House of Representatives  Legislative Endor...