Al’ummar Hausawa musamman wanda suke zaune a cikin birnin garin Jos ta arewa, sun kasance masu bada gudumawa wajen cigaban jahar Filato a fani daban daban kama daga kasuwanci, zamantakewa, hada har da siyasa, amma babban abun tamabaya anan shine ko shin su al’ummar ina suka dosa, ko muce ina tasu tsayar su a siyasar dubu biyu da ashirn da uku (2023).
Amma bari muyi duba da irin gudumawar da suka bayar wajen kafuwar gwamnatin Lalong
IRIN GUDUMAWAR DA SUKA BAYAR WAJEN KAFA GWAMNATIN LALONG
A sheharar dubu biyu da goma sha biyar al'ummar Hausawan garin Jos suka bada gudumawa sosai wajen kafa gwamnati maici a karkashin Rt. Honorable Simon Lalong inda suka bashi kuri’a mafi tsoka wanda ku shi, Gwamnan naji shi ya sha fadin cewa badan kuri’ar suba da laile ba zai kawo gaci ba. inda kuma yayi alkwarin saka masu da romon demokaradiyya.
Ko shin ya saka masu? Bari muyi duba da irin alkawarin da ya dauka masu kafin hauwar sa mulki.
1. GYARA BABBAR KASUWAR TERMINUS
A yayin da yake neman kujerar gwamna a 2015 Simon Lalong yayi alkwarin cewa zai gyara ita wanna kasuwa, domin kasuwanci ya bunkasa tare da rage rashin aikin yi, amma tun bayan da ya hau kan karagar mulki ba wani abu zo a gani da za'a ace an sake ji mai inganci game da gyara kasuwar, sai dai a wani lokacin da ake daf da zaben 2019, Gwamna Lalong ya waiwaye ita wannan kasuwa inda ya fadawa al’ummar Jos ta arewa cewa yanzu an gama komai da wanda zasu gyara kasuwar har an ware Naira Biyon Daya wajen rusa kasuwar.
Amma tunda aka rusa wani yanki na kasuwar har yanzu ba ko motar kasa daya da aka kawo, sai dai ma zargin gwamnatin Lalong da salwantar da karafen da aka cire a yayin rusa wani ban gare na kasuwar.
Amma kuma acikin shekarar 2022 aka kara jin cewa wai Gwamnatin jahar filato tare da hadin gwiwar bankin muslunci wato Jaiz zata gyara kasuwar wanda har yazu ba a sake ji ko ina maganar ta kwana ba.
Zamu iya cewa dai kawai gwamantin Lalong tayi kokari wajen yaudarar al’ummar Jos musamman hausawa wajen neman kuri’ar suba tare da ta cika masu wannan alkawarin ba.
A hira da mukayi da wasu mazauna kasuwar sun nuna cewa tabbas da za’a gyara wannan kasuwar da ta kawo cigaba ma jahar Filato da ma kasa baki daya, amma sun danganta kin gyarawar da baya rasa nasaba da kabilanci duba da yarda cewa su hausawan sune mafi amfana da wannan kasuwa.
2. BUNKASA CIKIN BIRNIN JOS
Wani daga cikin alkwarin da gwamnatin APC mai mulki tayi wa al’ummar Hausawan Jos shine bunkasa cikin garin da hanyoyi tare da kuma kara fadin garin, amma bisa dukkan alamu dai wannan alkawarin shima yana kokarin zama tarihi kamar yarda sauran yan siyasa suke ma jama’a. Domin zamu iya cewa banda titin Anguwan rogo wanda shima kasa da kilomita shida da ya dauki gwamnatin sama da shekara biyu kafin ta kammala ba wani abun azo a gani da za’ace ta aiwatar ma al’ummar Hausawan Jos. A lokacin da damuna take kara kusantuwa acikin garin Jos yana kasancewa mafi kazanta a duk sanda akayi ruwan sama, domin bayan ruwa ya sauka manyan titunan garin kan cika da shara da sauran datti dake barazana ga lafiyar yanki.
Bayan nan wanda ya bar garin Jos shekara ashirn idan ya dawo zai iya kama hanyar zuwa gida domin kuwa yarda yabar garin hakan zai dawo ya same sa ba tare da wani alamun samun chanji ba, akan hanyiyoyi.
Allah ya kyauta. Amma dai kam ya kamata alumma su lura wajen zaben shugabani
ReplyDeleteMaganar Mai magana ta farko Mai rubutu Yakoma baya lokachin da akeneman afara gyara Mai mutanen gari suke Chewa,har zanga zanga sukayi SUNA fadin basu yarda ba.
ReplyDeleteUbangiji Allah ya kyauta, kuma yasa mu matasa mu gane yancinmu a koda wannane lokaci kuri’armu yancinmu
ReplyDeleteWllhi especially government school, primary school , & secondary school, wllhi kullum yau I jiya, education system nothing nothing
ReplyDelete