Majalisar dattijan Nigeria, sun tafi hutu a yau Laraba,
domin samun cigaba da gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓe a jam'iyyun da suke
ciki, don tunkarar babban zaɓen shekarar 2023, kamar yadda shugaban majalisar,
Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana yayin zaman majalisar na wannan rana.
Lawan yace zace zasu tafi hutun ne domin tabbatar da abubuwa
sun zama cikin tsari a ƙasar nan, kuma za su dawo a ranar 28 ga watan Fabrairu,
kwanaki uku kenan bayan an gudanar da zaɓen shugaban ƙasa dana yan majalisun
tarayya, kafin su sake tafiya wani hutun a ranar 1 ga watan Maris, domin
gudanar da zaɓen gwamnoni da yan majalisun dokokin jiha, da za'ayi a ranar 11
ga watan Maris.
Cikin jawabinsa, Lawan yayi kira ga hukumar zaɓe mai zaman
kanta ta ƙasa INEC, da kuma jami'an tsaro, akan su tabbatar sunyi ayyukansu
yadda ya dace, domin yin zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana, karbabben zaɓe
kuma sahihi.
Majalisar Nigeriya |
Allah ya kyauta
ReplyDelete