Gwamnan jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya ce zai ɗaukaka ƙara game da hukuncin da kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta yanke, inda ta soke zaɓen da aka yi masa a matsayin gwamna.
Acikin martanin da ya yi ta hannun mai magana da yawunsa, Mallam Olawale Rasheed, Adeleke na jam’iyyar PDP
ya bayyana hukuncin kotun a matsayin kuskure.
Ya ce lamarin rashin adalci ne, wanda ya ci karo da muradin mafi yawan al’ummar jiohar.
A ranar jumu’ar nan ne kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe ta soke zaɓen da aka yi wa Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin gwamnan jihar Osun.
Kotun ta kuma ce tsohon gwamnan jihar, Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC ne ya lashe zaɓen idan aka yi la’akari da yawan ƙuri’un da aka kaɗa bayan kawar da ƙuri’un da aka yi aringizo.
A lokacin da yake yanke hukuncin, Mai shari’a Tetsea Kume, ya ce Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, INEC ba ta bi tanade-tanaden dokar zaɓe da na Ƙundin tsarin mulki yadda ya kamata ba.
A cewar kotun, idan aka cire ƙuri’un da ake zargin an yi aringizo, Adegboyega Oyetola na APC ya samu yawan ƙuri’u 314,921 yayin da Ademola Adeleke na PDP ya samu ƙuri’u 290,266.
Gwamna Adeleke ya buƙaci magoya bayansa su kwantar da hankalinsu, kuma a cewar sa, har yanzu shi ne halastaccen gwamnan jihar.
Comments
Post a Comment