Daga
Haruna Umar,
Ga dukkan alamu, shekarar 2022 ita ce shekarar ƙarshe da yaron talaka a Najeriya zai tafi ƙaro karatu a jami'a (University), ganin yadda wasu takardu masu alaƙa da wasu daga cikin jami'oin ke nuna yadda a ke shirin ninka kuɗin makaranta, ko ma dai na ce an ninka!
Ta iya yiwuwa wannan lamari ya na da alaƙa da artabun da ke tsakanin gwamnati da malaman jami'o'i. Ko ma dai menene, da gwamnati da ku malamai, ku tuna fa wannan danbartuwa ta ku a kan ƴaƴan talakawa ta ke ƙare wa. Ta na ƙare wa ne a kan mutanen da su ke neman na sa wa a baka, kafin nan komai.
A ranar 14 ga watan Fabrairun 2022, ƙungiyar malaman jami'o'i ta ƙasa, ASUU, ta shiga yajin aikin gargaɗi bayan ta zargi gwamnatin Najeriya da ƙin cika ma ta alƙawura da ta ɗauka. Bayan tsahon lokaci, wannan lamari ya sanya ƙungiyar ta yi ta zama da wakilan gwamnati. Wani lokaci a rabu ‘baran-baran’, wani lokaci kuma a rabu a na yaƙe (murmushin da bai kai har zuci ba).
Shigar ƙungiyar ASUU yajin aiki ya sanya gwamnatin tarayya a ƙarƙashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ƙin biyan malaman jami'o'i kuɗaɗen su.
Dalili kuwa shi ne tabbatuwar tsarin nan na “NO WORK NO VOTE", ma'ana, ba bu biya idan ba'a yi aiki ba. Wannan mataki ya sanya ƙungiyar ASUU ci gaba da zaman gida har sai da ƴaƴan ƙungiyar su ka kwashe watanni bakwai a zaune, lamarin da wasu ke ganin ya yi sanadiyar mutuwar wasu daga cikin malaman jami'o'i, wasu kuma sun shiga halin matsi.
Bayan cikar ƙungiyar ASUU watanni bakwai ta na yajin aiki, kakakin majalisar wakilai, Rt. Honourable Femi Gbajabiamila, ya yi nasarar sasanta ɓangarorin biyu, lamarin da ya sanya shi yin fice a faɗin Najeriya, la'akari da cewa waɗanda abin ya shafa, kamar ministan ilimi, Malam Adamu Adamu da ministan ayyuka da ɗaukar ma'aikata, dakta Chris Ngige sun gaza shawo kan lamarin.
Daga ƙarshe dai ASUU ta janye yajin aikin na wucin gadi a ranar 14 ga watan Oktoban 2022, bayan wata 8 dai-dai kenan da shigar ta yajin aikin. Allah Ya saka wa Rt. Honourable Femi Gbajabiamila da alkairi a bisa jajircewan da ya yi na sasanci tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya. Wannan a ɓangaren gwamnati da malamai kenan.
Idan na dawo ɓangaren ɗalibai kuma, tsawon lokacin da su ka kwashe a gida sun yi hutu ne cikin fargaba da tunanin cewa a ko wani lokaci za su iya koma wa makaranta. Wannan tunani ya sanya da dama daga cikin ɗalibai ƙin kama sana'o'i saboda su na gudun kar su fara aiki kuma ASUU ta janye yajin aiki.
Mai karatu zai iya cewa “to ai wannan ba shi ne karon farko da ASUU ta tafi yajin aiki ba", to amma duk da haka, ko wani yajin aiki da yadda ya ke kasancewa.
Yajin aikin ASUU ya shafi ɗaliban jami'o'i fiye da duk wani mai ruwa da tsaki a harkar ilimi! Ɗalibin da ya kamata a ce ya kammala karatun sa na digiri a shekaru hudu ba ya samun damar hakan. Sai ka ga a maimakon shekaru huɗu, mutum ya kwashe shekaru shida ko fiye da hakan (ya danganta da yanayi na cin jarabawa ko akasin haka).
Bayan ƙarin wa'adin karatu, ɗalibai da dama da su ke da burin mallakar shaidar kammala jami'a sun haɗu da ajalin su. Wasu sun mutu a sanadiyar baƙin cikin yajin aiki, wasu kuma sun mutu a sanadiyar neman na jefawa a baki tunda dai ba makaranta (duk da cewa kowa ba ya wuce ajalin sa).
Masu raunanan zuciya sun yi amfani da raunin su wajen kwashe wa ɗalibai kayayyaki da su ka bari a ɗakunan kwanan ɗalibai kafin su tafi yajin aikin da ba su da damar sa wa a yi ko su hana. Allah Sarki. Ɗalibi, bawan Allah! Idan za ka tashi hankali sai a ce kai mai ilimi ne. Allah Ya yi wa ilimin ka albarka. Amin.
Bayan dukkan waɗan nan ƙalubale da ɗalibai su ka fuskanta, sai ga shi a kwanakin nan wasu daga cikin manyan jami'o'in ƙasar nan sun fara fitar da sabbin tsare-tsaren biyan kuɗi. Wasu makarantu sun ƙara kaso kaɗan, yayin da wasu kuma suka ninka kuɗin da hankali ma ba zai ɗauka ba. Wannan lamari ya tayar da hankalin duk wani ɗalibi, musamman ma wanda ya fito da ga gidan da ba su da ƙarfi. Da yawa da ga cikin ɗalibai sun shiga fargaba, inda wa su da dama ke tunanin ko da akwai yiwuwar su ciga da karatu ko kuma su haƙura, su ajiye. Allah Ya keɓo bayi.
Wannan dalili ya sanya ni zanta wa da wasu al'umma da suka haɗa da ɗalibai da masu riƙe da ragamar gida, inda su ka tabbatar min da halin da su ke ciki.
“ Wata rana mu na zaune bayan an gama darasi, wani daga cikin malaman mu ya kunna wayar sa, sai ya nuna ma na sabon jadawalin kuɗin makaranta da za mu riƙa biya nan gaba kaɗan,” cewar wani ɗalibi da ya fito daga ɗaya daga cikin jami'oin gwamnatin tarayya a shiyyar Arewa maso Gabas.
“Ni na ke ɗaukar nauyin karatun ƙanne na. Zan sa ƙani na ƙwaya ɗaya a sabuwar makarantar koyon aikin likitan ci da a ka buɗe a ƙaramar hukumar mu, amma abin ya fi ƙarfi na. Yanzu mun haƙura,” cewar wani yaya da ya yi ƙoƙarin kai ƙanin shi jami'a.
Shi kuwa wani uba cewa ya yi “ Na yi burin na kai ƴa ta makarantar gaba da sakandiri, to amma na ga abin ba mai yiwuwa ba ne. Yanzu na bar wa Allah komai. Ina addu'ar Allah Ya ba ni yadda zan yi na aurar da ita kawai."
Yanzu dai shekarar 2022 ta zo ƙarshe. Al'ummar duniya na shirye-shiryen shiga sabuwar shekara ta 2023. Al'ummar Najeriya, musamman ɗalibai na fargabar shiga sabuwar shekarar, Kasancewar ba su san da wani salo shekarar za ta zo mu su ba. Shin akwai yiwuwar ASUU ta ƙara shiga yajin aiki? Shin dukkan jami'o'i za su huce haushin su ne ta hanyar ƙara wa ɗalibai kuɗin makaranta? Ko dai wani dalili zai zo da zai sa waɗannan matsaloli ba za'a sake fuskantar su ba? Koma dai menene, fatan mu shi ne Allah Ya sa daga shekarar 2022 matsalolin da su ke addabar fannin ilimi sun zo ƙarshe. Allah Ya sa ɗalibai za su samu damar sararawa a sabuwar shekarar da za'a shiga. Allah Ya zaunar da kowa lafiya a Najeriya da duniya baki ɗaya. Allah Ya sa a gudanar da zaɓukan Najeriya lafiya, Ya kuma bai wa Najeriya shuwagabanni na gari.
Da ga ƙarshe, Ina mai amfani da wannan dama wajen yin kira ga shugaban ƙasa mai shirin barin gado, shugaban ƙasa mai rabo a babban zaɓen shekarar 2023, ministocin da abin ya shafa masu ci, ministocin da abin ya shafa ma su zuwa, dukkan ƴan majalisu, hukumomin kula da karatu a dukkan matakai, hukumar kula da karatun jami'a, shuwagabannin jami'o'i da malaman su, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilimi, a ji koken talakawa, a taimaki fannin ilimi, kana a yi duba a kan batun ƙara wa ɗalibai kuɗaɗen makaranta, domin hakan zai iya sanadin ajiye karatun da yawa daga cikin ɗalibai.
Haruna Umar,
ibnumar613@gmail.com
07062579831
Comments
Post a Comment