Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta ba da umarnin kamo wani dan Burtaniya, James Nolan saboda ya keta sharuddan beli.
Mai shari'ah Ahmed Mohammed ne ya ba da umarnin bayan James Nolan wanda darakta ne a kamfanin Process and Industrial Development Limited (P&ID) ya gaza bayyana a gaban kotu.
Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ce ta shigar da James kara tare da kamfanin Lurgi Consult Limited da sauran wasu, a wata shari'a da ta shafi halasta kudin haram kimanin dala biliyan 9.6.
Da yanke ba da hukunci, Mai shari'ah Ahmed Mohammed ya ce James ya karya sharuddan belin da kotu ta ba shi, don haka kotu ta soke belin kuma ta fitar da sammaci don a kamo shi, duk inda ya shiga.
Tashar talbijin ta Channels ruwaito alkalin na kuma umarci mutumin da ya tsayawa James Nolan ya bayyana a gaban kotu lokacin zaman kotu na gaba, don ya yi mata bayani a kan dalilin da ya sa kotu ba za ta karbe takardun lamuni da ya ajiye a kotu ba.
Comments
Post a Comment