Chelsea ta kori kocinta, Thomas Tuchel bayan kashin da kungiyar ta sha a ranar Talata a Gasar Zakarun Turai.
Kocin mai shekara 49 wanda ya taɓa jagorantar Borussia Dortmund da Paris St-Germain zai bar Stamford Bridge bayan wata 20 da kama aiki.
Mai kulob ɗin, Todd Boehly ya bayyana cewa, mataimakan Tuchel ɗin za su ci gaba da aikin horaswa har sai an samu wanda zai maye gurbinsa.
Wata sanarwa da masu kulob din suka fitar sun ce, suna ganin lokaci ya yi da za a kawo wani sabon babban koci.
An naɗa Tuchel a matsayin koci a ranar 26 ga watan Janairun 2021, bayan ya maye gurbin Frank Lampard, inda ya kai kulob ɗin ga samun nasarar su ta biyu a gasar Chmpions League wata huɗu bayan ya shiga kulob din.
Bayan nan sai ya ƙara da cin Uefa Super Cup da kuma Fifa Club World Cup duk a shekarar.
Comments
Post a Comment