Jami'an jihohi na wata kungiya me suna ATIKU/OKOWA VANGUARD 2023, sun ce Dan Takarar shugabanci kasa na PDP Alhaji Atiku Abubakar nada dukkan kwarewar da ake bukata domin ceto Najeriya tare da sauya al'amuran jama'a domin su koma daidai.
Wakilan wannan kungiya sun ce suna da wannan tabbaci saboda irin tarihin gogayya da kwarewar da Atiku yake da ita a harkar kasuwanci da shugabancin jama'a.
Babbban daraktan kungiyar Hon. Sam Amonu Lokacin da ya jagoranci kungiyar zuwa ziyara ga Atiku, yace tsohon mataimakin shugaban kasar shi ne zabi Mafi dacewa domin kubutar da Najeriya Daga halin da take ciki.
Ita ma a nata bangaaren, shugabar kungiyar ta kasa Dr (Mrs) Obi Nwaogu tace manufar ziyarar ita ce isar da godiyarsu ga Atiku Abubakar a kokarin da yake na karfafa tsarin dimukuradiyya a Najeriya.
Tace suna da kyakkyawan fata akan Atiku da Okowa domin gwamnatin su zata ceto Najeriya.
Comments
Post a Comment