Dakarun tsaro na can suna neman 'yan bindigar da suka kashe sojojin Najeriya a kalla biyar cikin jihar Anambra, da ke kudancin kasar.
Zuwa yanzu babu wata kungiya da ta fito ta ce ita ce ke da alhakin kai wannan hari na ranar Laraba a Umunze kusa da fitacciyar kasuwar Nkwo.
Sai dai hukumomi a kasar sun sha zargin kungiyar IPOB da kaddamar da hare-hare kan cibiyoyin gwamnati da jami'an tsaro a Anambra da ma sauran jihohin kudu maso kudu.
Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya yi tur da wannan kisan gilla.
Ya kuma ce dole ne a farauto wadanda suka aikata mummunan aiki tare da hukunta su.
Comments
Post a Comment