Wani lauya Mai zaman Kansa a Jihar Kano baa rrister Badamasi sulaiman Gandu yayi barazanar gurfanar da Hukumar hisba agaban Kotu Idan Bata ɗauki mataki akan Ado gwanja ba nan da kwanaki
Lauyan Wanda ya Mika takardar korafi ga Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje khadimul Islam ta hannun Ofishin sakataren Gwamnatin Kano.
Cikin takardar korafin da Barrister Badamasi sulaiman Gandu ya aikewa Gwamnan, ya Nemi Gwamnatin Kano ta ɗauki matakin Gaggawa akan wata Waka da Wani mawaki anan kano Mai Suna Ado Gwanja yayi Mai Suna (Cas ko Kuma asosa)
Baya ga Ofishin Gwamnan Kano barrister Badamasi sulaiman Gandu ya Kuma Mika irin wannan korafi ga Hukumar hisba ta Jihar Kano da Kuma Hukumar tace fina finai da dab'i akan daukar matakin ladaftar wa ga mawaki Ado Gwanja.
Acewarsa Jihar Kano tana da tsari na mutunta addini da Kuma Tarbiya sai Gashi Wani mawaki Yana wargaza Tarbiyar ya"Yan Jihar Kano ta Hanyar yin wakar da ta Saba da Tarbiya da Kuma addini.
Barrister Badamasi sulaiman Gandu ya Roki wadanda ya Mika wannan korafi Garesu da su gaggauta daukar matakin Hana Fitar da wakar da Kuma ja Masa kunne saboda abunda yakira ya sabawa addini da Kuma Tarbiya.
Acewar lauyan amatsayina na Dan Kano Mai Kuma kishin addinina na musulunci Bai kamata nayi shiru akan wannan wakar ta Ado gwanja ba.
Comments
Post a Comment