![]() |
| Marubuci: Abba Abubakar Yakubu |
Daga Abba Abubakar Yakubu
Wani sabon salon yaƙin neman zaɓe da ýan siyasa a Nijeriya suka ɓullo da shi shi ne na amfani da wasu gungun matasa wajen taimaka musu yaɗa manufofinsu da taya su neman goyon bayan jama'a ta hanyar amfani da zaurukan sada zumunta a kafafen sadarwa na zamani.
Raja'ar da mutane suka yi wajen mu'amala da waɗannan zaurukan sada zumunta irin su Facebook, Twitter, Instagram da WhatsApp da sauran su da dama ya sa harkokin sadarwa da isar da saƙonni ba na abokai da ƙungiyoyin matasa kaɗai ba, hatta kafafen sadarwa, ma'aikatu da hukumomin gwamnati sun bi sahu, wajen buɗe shafuka da zauruka daban daban, don isa ga jama'a, tattaunawa da muhawara kan ayyukan su.
Ýan siyasa na amfani da waɗannan matasa ne saboda jan hankalin sauran jama'a su fahimci tsare tsaren su da manufofinsu na siyasa, musamman kasancewar matasan su ne suka fi mu'amala da waɗannan shafuka, saboda abubuwan da tsare tsaren manhajojin ke ba su na nishaɗi, musanyen saƙonni na abokantaka, soyayya, da ɗebe kewa.
Sakamakon yadda akasarin waɗannan matasa ke zaune babu ayyukan yi, ko babu wasu nauye nauye a kansu da za su ɗauke musu hankali, ko kuma dai ɗalibai ne da harkar karatu ta tsaya, saboda yajin aikin malamai ko kuma rashin wadatar iyaye.
Wannan yana ƙara nuna irin yadda ýan siyasa ke bin kowacce hanya don ganin sun cimma burin su. A baya an ga yadda ýan siyasa suka riƙa amfani da matasa wajen ba su kayan shaye shaye suna yi wa kansu illa da sunan bangar siyasa, ana tura su tarwatsa cibiyoyin zaɓe, satar akwatin zaɓe da kisa ko yi wa abokan adawa lahani. Mun ga yadda ýan Jagaliyar siyasa a Kano, ýan Kalare a Gombe, ýan Gunda a Bauchi da ýan ECOMOG a Borno suka haifar da babban ƙalubalen tsaro a jihohinsu, wanda har yanzu ba a kammala warware wa ba.
Za a iya cewa, wannan salo na amfani da soshiyal midiya ya kawo sauyi a harkar jagaliyar siyasa, inda yanzu harkar ta koma bayan fage ake yin ta a wayoyin hannu ba tare da makami ko shaye shaye ba. Sai dai kuma wasu na cewa, alƙalami ya fi takobi kaifi. Amfani da kalaman ɓatanci, cin zarafin juna, yaɗa labaran ƙarya don lalata kima da mutuncin wani ɗan siyasa ko abokin adawa, ita ma illa ce babba, da ke da haɗari ga ci gaban al'umma da zaman tare.
Babu wani ɗan siyasa yanzu da za ka ga ba shi da wasu rukunin matasa da ya ware yana basu wasu ýan kuɗaɗe suna sayen data don taimaka masa wajen yaɗa manufofinsa, inda kuma za ka ga wani lokaci har da tayar da muhawara mai zafi tsakanin magoya bayan wannan ɗan takara zuwa wancan. Kowanne ɓangare na fifita ɗan takarar da suke goyon baya, ko dai saboda wasu ayyuka da ya yi wa jama'a a baya na ci gaba, ko yawan muƙaman da ya riƙe a baya da gogewarsa, ko yadda yake nuna kishin sa ga jama'ar yankin sa, addinin sa ko tallafawa matasa da ayyukan yi.
Waɗannan na daga cikin abubuwan da akasari aka fi amfani da su wajen yaƙin neman zaɓe a zaurukan sada zumunta. Kuma hakan a ra'ayin wasu matasan ýan siyasa yana tasiri sosai, kuma kwalliya na biyan kuɗin sabulu, musamman idan aka yi dace da gwanayen iya rubutu da mayar da martani ga duk wani motsi na abokan adawa, wanda kuma yake da mabiya ko abokai da dama, ta yadda da zarar ya tura saƙo ɗaya cikin ýan mintina ƙalilan zai jawo muhawara da tattaunawa a kai.
Usman Bigi yana daga cikin matasan da suke wannan aiki na siyasar soshiyal midiya, ya kuma bayyana min cewa babu shakka ana samun alheri kadaran kadahan, amma yawanci matasa sha'awa ce take kai su ga shiga wannan harka saboda suna son su ma a riƙa damawa da su, musamman idan kakar zaɓe ta zo, don kada a yi babu su.
Shi kuwa Bala Sawaba matashin ɗan siyasa ne da ko da yaushe za ka same shi a gidan wannan ɗan siyasa zuwa wancan, yana abin da ake cewa kala, shi da wasu abokan sa, don samun na sayen data, da shiga cikin manyan ýan siyasa ana tattauna hanyoyin cin nasarar zaɓe da nakasa tasirin abokan adawa. A ganin sa duk wani matashi da yake da burin yin siyasa to, dole ne ya zama yaron wani, don ya koyi dabarun siyasa, ya samu gogewa kuma a san shi sosai a harkar.
Ummu Ayman matashiya ce da ake gogawa da ita a wannan fage a cikin mata ƙalilan da suke ba da gudunmawa wajen muhawara kan ýan siyasa a zaurukan sada zumunta ta yi fatan ýan siyasa ba za su manta da su ba bayan samun nasarar zaɓe, domin yabawa da irin rawar da suka taka. A maimakon ko da yaushe a bar su da tura mota tana tashi ta buɗe su da hayaƙi, ba za a sake waiwayar su ba sai wani zaɓen ya zo.
A dalilin haka ne, wani matashin ɗan siyasa a Jos, Malam Abdulhadi Abdullahi ya fito da wani salon jan hankalin matasa inda yake kiran matasa masu siyasar soshiyal midiya su tabbatar sun mallaki katin zaɓen su a hannu, domin ranar zaɓe su yi amfani da shi wajen kawo sauyin da suke da burin gani a siyasar yankin su. Kuma da alamun wannan salo nasa yana samun karɓuwa, a wajen wasu matasan.
Masu hikimar magana dai na cewa, zamani riga ne. Allah kuma shi ne zamani. Babu wanda zai yi faɗa da abin da zamani ya kawo, amma kuma ba zai yiwu a yi shiru a kawar da kai ba, akwai buƙatar matasa su samu jagoranci da saiti kan yadda za su tafiyar da wannan harka ta soshiyal midiya da kaucewa haɗarin ta. Don ya kasance ba a fagen siyasa kaɗai ba har a sauran harkokin su na rayuwa zai zama musu mai amfani.
Amma a lokaci guda kuma ya zama wajibi a tunatar da matasa cewa, Facebook ko Twitter da WhatsApp ba Jam'iyyar siyasa ba ce, kuma ba katin zaɓe ko rumfar zaɓe ba ne, dole in suna buƙatar yin siyasa sosai, su je su yi rijista da wata jam'iyyar siyasa da suka aminta da tsarin ta da manufofin ta, kuma su tabbatar suna da katin zaɓe a hannun su, don ya zama makamin su na kawo sauyi a al'amarin rayuwar su da al'ummar su.
Sannan kuma su tabbatar sun koma makaranta ko kuma sun kammala Karatun su, ta yadda ko da taimaka musu wani ɗan siyasa zai yi, zai yi musu taimakon da zai inganta rayuwar su ne, wajen sama musu aikin da ya dace da wahalar da suka yi masa ta yaƙin neman zaɓe, masu sana'o'in dogaro da kai kuma su dage wajen riƙe sana'o'in su, da mutunci, kada su bari siyasa ta ɗauke musu hankali daga abin da yake tsare mutuncin su, da tallafawa iyalan su. Domin duk wani abu da za su samu daga wani ɗan siyasa, ba wani abu ne da ya kai ya kawo ba.
Har wa yau kuma ina mai ba da shawara, a yayin da ake tattaunawa game da gudunmawar ýan siyasa a riƙa kawo batutuwa masu muhimmanci da za a riƙa ƙalubalantar ýan siyasa a kai, abubuwan da za su kawo wa al'umma cigaba da makoma ta gari. A maimakon a yi ta zuga su ana yabawa ayyukan da suka yi na neman suna ko son a sani, ba na tsakani da Allah ba, a mafi akasarin lokuta!
A kaucewa rubuce rubucen hassala juna ko tsokano fitina don a ci zarafin wani ko aibata shi. Abin da ka iya haifar masa da mummunan suna da lalata mutuncin sa ba kawai a siyasance ba, har ma da martabar sa a idon al'umma da ta iyalan sa.

Comments
Post a Comment