Skip to main content

Romon Baka Gwamnati Ke Mana Don Haka Babu Gudu Babu Ja Da Baya A Kan Yajin Aiki – ASUU

 




Ƙungiyar malaman jami’a a Najeriya ASUU ta ce gwamnatin Najriya ba ta shirya kawo ƙarshen yajin aikin da su ke ciki ba.

ƙungiyar ta alaƙanta hakan da abin kunya sakamakon shafe kusan watanni shida su na yajin aikin amma gwamnatin ta gaza kawo ƙarshen sa.

Shugaban ƙungiyar Emmanul Osodoke ne ya sanar da haka a wani shiri da aka gabatar tare da shi a gidan talabiji na Channels.

Ya ce romon baka gwamnatin ke yi wa ƴan ƙasar amma babu wata cikakiyar matsaya da ta ɗauka don ganin an kawo ƙarshen yajin aikin.

Ganin yadda al’amuran ke tafiya, shugaban yace ba za su gajiya ya sa su janye daga yajin aikin da su ke ciki ba har sai an dawo da ƙimar karatu a mkarantun jami’a.

Ya ƙara da cewa a shirye su ke su tabbatar sun koma bakin aikinsu muddin aka cika musu alƙawuran da su ke nema daga gwamnatin.

Shugaban ƙungiyar ya ce gwamnati ba da gaske ta ke ba don ganin ta kawo ƙarshen yajin aikin da su ke ciki.

Fiye da watanni shida ƙungiyar ta fara yajin aiki domin neman biyan buƙatunsu daga gwamnatin wanda hakan ya haifar da tsaiko ga karatun ɗaliban jami’a.

Comments

Popular posts from this blog

Bridging Digital Divides: Empowering People with Special Needs and Uniting Communities Through Technology

By Abdullahi Abdulhafiz Aliyu In today’s fast-changing digital landscape, access to technology is no longer a luxury—it is a necessity. Yet, for millions of Nigerians, especially people with special needs, the digital world remains out of reach due to systemic barriers and a lack of inclusive learning opportunities. My work as a journalist and digital advocate has focused on breaking these barriers, ensuring that technology serves as a tool for empowerment rather than exclusion. Through my engagement with individuals with disabilities and as the host of Duniyar Fasaha (Fasaha World) on Unity FM, I have worked to bridge the digital divide by providing foundational digital education to marginalized groups. By introducing people with special needs to basic computer skills such as Microsoft Word, Excel, PowerPoint, and internet navigation, I have witnessed firsthand how technology can unlock new opportunities and transform lives. Digital Skills for Special Needs: A Path to Inclusion Inclu...

Yanzu yanzu: 'yan majalisar dattijai sun tafi hutu domin gudanar da yaƙin neman zaɓe

Majalisar dattijan Nigeria, sun tafi hutu a yau Laraba, domin samun cigaba da gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓe a jam'iyyun da suke ciki, don tunkarar babban zaɓen shekarar 2023, kamar yadda shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana yayin zaman majalisar na wannan rana. Lawan yace zace zasu tafi hutun ne domin tabbatar da abubuwa sun zama cikin tsari a ƙasar nan, kuma za su dawo a ranar 28 ga watan Fabrairu, kwanaki uku kenan bayan an gudanar da zaɓen shugaban ƙasa dana yan majalisun tarayya, kafin su sake tafiya wani hutun a ranar 1 ga watan Maris, domin gudanar da zaɓen gwamnoni da yan majalisun dokokin jiha, da za'ayi a ranar 11 ga watan Maris. Cikin jawabinsa, Lawan yayi kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, da kuma jami'an tsaro, akan su tabbatar sunyi ayyukansu yadda ya dace, domin yin zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana, karbabben zaɓe kuma sahihi. Majalisar Nigeriya

All Is Set For APC Presidential Primary.

All is now set for the All Progressives Congress (APC) Presidential primary in Abuja holding from Monday, June 6 to June 7 at the Eagle’s Square with six aspirants in the lead, Jasawa Times learned. The presidentail aspirant include the Vice-President Yemi Osibanjo; former Minister of Science and Technology, Ogbonnaya Onu, Ebonyi Gov. Dave Umahi; former Lagos Gov. Bola Ahmed Tinubu, former Minister of Transportation, Rotimi Amaechi and ex-Minister of State for Education, Chief Chukwuemeka Nwajiuba. The Eagles Square is expected to host about 2,240 delegates from the 36 states and the Federal Capital Territory. Expectedly, the influx of people into the FCT has increased, a development that has attracted more police presence at the Eagles Square and some hotels hosting the delegates and chieftains of the APC. Ahead of the event, the party’s National Chairman, Sen.Abdullahi Adamu on Sunday visited the Eagles Square where he expressed satisfaction with the facilities put in place by...