A jiya Asabar, shugannin kungiyar manoman shinkafa da masu sarrafata da kuma masu sayar da ita ta kasa NARPPMMAN sun kai ziyarar goyon baya zuwa ga dan takarar shugabancin Najeriya na Jam'iyyar PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar a gidan sa dake Abuja.
Jagoran tawagar Alhaji Ahmadu Mustapha yace manufar ziyarar ita ce taya murna ga Wazirin Adamawa bisa nasarar da ya samu a zaben fitar da gwani na Jam'iyyar PDP.
Ya yi alkawarin cewar kungiyar zata mara baya tare da kasancewa masu biyayya ga dan takarar, inda ya Kara da cewa mambobin kungiyar sama da mutane miliyan Daya sun yanke shawarar marar baya ga Atiku, saboda yadda yake zuba jari a bangaren noma, inda suka ce sun gamsu Atiku Shima manomin shinkafa ne.
Da yake mayar da jawabi, tsohon mataimakin shugaban kasar ya godewa kungiyar bisa wannan ziyara, inda ya ce yana cikin harkokin noma tsundum tun daga Shekara ta 1984 tun ma kafin a kafa wannan kungiya.
Comments
Post a Comment