LALONG YA CE KASANCEWAR SHI JAGORAN YAKIN NEMAN ZABEN MUSULMI DA MUSULMI BAI DA ALAKA DA ADDININ SHI
Gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong a ranar Laraba, ya kalubalanci kiristocin da suka Ki amincewa da mukamin da ya samu na jagorantar tawagar yakin neman zaben dan takarar shugabancin kasa na APC, inda ya ce a matsayin Shi na dan katolika Wanda ya samu babban kambun yabo, Hakan bai nuna cewa abinda yake yi ba daidai bane.
Tun daga lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya zamto dan takarar shugaban kasa na APC, tsohon gwamnan jihar Legas din ya zabi tsohon gwamnan jihar Borno a matsayin abokin takarar Shi.
Tun daga nan kuwa wannan mataki na Tinubu ya rika janyo cecekuce, musamman daga bangaren kiristoci da kungiyar kiristoci ta kasa, CAN, wacce tuni taki amincewa da takarar musulmi da musulmi.
To amma gwamna Lalong ya gamsu, inda ya goyi bayan wannan tafiya ta musulmi da musulmi, bayan Sun gana da shugaban kasa Buhari a fadar gwamnatin tarayya a Abuja.
A Wani taron tambayoyi da bayar amsasoshi da aka gudanar, Lalong ya ce zai cigaba da Zama cikakken dan katolika, duk da matsayin da aka bashi a yaƙin neman zaben musulmi da musulmi.
Gwamnan ya ce Yana matukar girmama addinin sa a matsayin shi na kirista, to amma duk da haka an zabe shi ya zama gwamnan mabiya duka addinai dama Wanda basu da addini ne.
Gwamnan daga bisani ya ce bai san ma ko daga Ina wadanda suke ikirarin cewa su kiristoci ne da suka Ki aminta da mukamin nashi suka fito ba, domin a cewar Shi, lokacin da yake dawowa Jos bayan karbo takardar matsayin da ya samu, kungiyar CAN reshen jihar Plateau ta kasance daga cikin wadanda suka je taro Shi.
Comments
Post a Comment