Za a bude hada-hadar siyasa gadan-gadan ranar 28 ga watan Satumba 2022. Daga wannan rana hukumar zabe ta bada izini a shiga kamfen. Ba za a tsaya ba sai ranar 23 ga watan Fabrairu 2023, wato saura kwana biyu a fara zaben shugaban kasa dana yan majalisar dattijai da na tarayya.
In kana son sanin yadda mutanen Najeriya za su yi zabe kuma wa za su zaba ga hanyoyi da za ka yi duba da la'akari da su guda biyar.
Na Daya;
Duba a Masallacin da kake sallar asuba, ko cocin da kake halarta, makotanka na gida a dama da hagu, gabas da yamma, shin zasu zabi APC, ko sauran jam'iyyun zasu zaba?
Na biyu;
Duba abokanka a kasuwa da wadanda kuke aiki tare a kamfanoni ko ofis dinku da wadanda kuke haduwa kullum wajen sana'a, mutum nawa ne zasu zabi APC, nawa ne zasu zabi sauran jam'iyyun?
Na uku;
Duba 'yan makarantarku ta Boko( wato jami'a da kolejojin ilimi da Polytechnics, masu yajin aiki da wadanda ke bakin aikinsu) da dalibai na zaure da majalisi islamiyya da duk gurin da kuke haduwa neman ilimi, mutum nawa ne zasu zabi jam'iyyar APC, nawa ne zasu zabi sauran jam'iyyun?
Na hudu;
Duba wadanda kuke mu'amala a filin wasa ko shakatawa da sharholiya, 'yan nishadi da yawo a duniya, su waye da waye a cikinsu zasu zabi APC, su waye kuma zasu zabi sauran jam'iyyun?
Na biyar;
Duba sosai a 'yan siyasar unguwarku a matakin cafta da mazaba da karamar hukuma da jiha har ma da kasa baki daya, su waye, suna iya tallan jam'iyyar APC ko sauran jam'iyyun?
Sakamakon da ka samu, shi ne hisabin da mutanen kasar nan suke kudirin aiwatar a ranar zabe. KAR KA YAUDARI KANKA
MALLAKIN RUBUTU BELLO MUHAMMAD SHARADA
Comments
Post a Comment