Skip to main content

Hukumar INEC tace ba ta da 'yan takarar Sanata a mazabun Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma daga APC

 Hukumar INEC tace ba ta da 'yan takarar Sanata a mazabun Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma daga APC




Har yanzu tsugene Bata karewa Sanata ahmad lawn da Kuma godswill akfabio ba, Domin kuwa Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta bayyana cewa Jam'iyya mai mulki a kasar, APC, ba ta da 'yan takarar Sanata a mazabun Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.

Shugaban Majalisar Dattawan kasar, Ahmed Lawan, mai wakiltar Yobe ta Arewa na fafutukar samun tikitin tsayawa takara karkashin Jam'iyyar APC bayan da ya sha kaye a zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta bayyana cewa Jam'iyya mai mulki a kasar, APC, ba ta da 'yan takarar Sanata a mazabun Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.

Shugaban Majalisar Dattawan kasar, Ahmed Lawan, mai wakiltar Yobe ta Arewa na fafutukar samun tikitin tsayawa takara karkashin Jam'iyyar APC bayan da ya sha kaye a zaben fitar da gwani na dan takarar shugaban kasa

Saidai Kwamishinan Hukumar zabe, Festus Okoye ya ce INEC ba ta da wani dan takarar APC da zai wakilci mazabun Yobe ta Arewa da Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.

A wata hira da Gidan Talabijin na Channels TV, Okoye ya kara da cewa "a mazabun biyu, an gabatar da sunayen mutum biyu kuma hukumar ta yanke hukuncin cewa mutanen ba su ne halastattun wadanda suka lashe zaben fitar da gwanin da APC ta gudanar ba kuma ba mu wallafa sunayensu ba".

Ya ce APC ta dora sunayen Lawan da Akpabio cikin jerin sunayen 'yan takara a shafin intanet na INEC amma hukumar zaben ta yanke hukuncin cewa mutanen biyu ba su ne aka tsayar da su ba a zaben fitar da gwanin Jam'iyyar.

A cewar Okoye, rashin wallafa sunayen mutanen biyu da bayanansu a karkashin mazabun na nufin zuw yanzu APC ba ta da sunayen 'yan takarar a mazabun biyu.

Ko a makon da ya gabata sai da INEC ta musanta sauya kwanan watan wasu takardu domin samun damar shigar da sunayen Lawan da Akpabio a matsayin 'yan takarar kujerar Sanata a babban zaben kasar na 2023.

INEC dai ta bayyana cewa ba ta wallafa foma-foman mutanen biyu ba - matakin da ya sa aka shigar da kara wadda kuma har yanzu take gaban alkali.

Hukumar zaben ta ce hakan ne ya sa ta yi watsi da duk wata dabara ta gabatar da takardun bogi da ke tabbatar da takarar mutanen biyu a daidai lokacin da maganar ke gaban kotu.

Comments

Popular posts from this blog

Bridging Digital Divides: Empowering People with Special Needs and Uniting Communities Through Technology

By Abdullahi Abdulhafiz Aliyu In today’s fast-changing digital landscape, access to technology is no longer a luxury—it is a necessity. Yet, for millions of Nigerians, especially people with special needs, the digital world remains out of reach due to systemic barriers and a lack of inclusive learning opportunities. My work as a journalist and digital advocate has focused on breaking these barriers, ensuring that technology serves as a tool for empowerment rather than exclusion. Through my engagement with individuals with disabilities and as the host of Duniyar Fasaha (Fasaha World) on Unity FM, I have worked to bridge the digital divide by providing foundational digital education to marginalized groups. By introducing people with special needs to basic computer skills such as Microsoft Word, Excel, PowerPoint, and internet navigation, I have witnessed firsthand how technology can unlock new opportunities and transform lives. Digital Skills for Special Needs: A Path to Inclusion Inclu...

Tragedy in Bukuru: Trader Killed, Two Injured in JMDB Task Force Operation

A tragic incident occurred in Bukuru, Jos South LGA, on Monday, resulting in the death of a trader, Nasiru Abubakar, and injuring two others. The incident happened during an enforcement operation by the Jos Metropolitan Development Board (JMDB) task force. The Nigerian Police Logo According to reports, the task force was attempting to disperse a group of criminal elements when a warning shot was fired, unfortunately hitting the trader. The incident also resulted in the destruction of several vehicles, with over five cars set ablaze. The Commissioner of Police, Emmanuel Adesina, promptly visited the scene to assess the situation, and normalcy has been restored. The police command has issued a stern warning to individuals with criminal intentions, urging them to desist from their activities or flee the state. 

Reps Approve Tinubu’s Emergency Rule Request for Rivers State

 The House of Representatives has approved President Bola Ahmed Tinubu’s request to impose a state of emergency in Rivers State following heightened political tensions and security concerns. The decision, made during a plenary session on Wednesday, comes after weeks of instability in the oil-rich state, where political clashes and reports of pipeline vandalism have raised national security concerns. Why the Emergency Rule? The crisis in Rivers State stems from an ongoing power tussle between Governor Siminalayi Fubara and state lawmakers, a situation that has escalated into widespread unrest. Reports also indicate that increased incidents of oil theft and pipeline vandalism are affecting Nigeria’s economic stability. President Tinubu, in his emergency rule proclamation, suspended Governor Fubara and other elected officials, appointing retired Vice Admiral Ibokette Ibas as the military administrator to oversee the state’s affairs. House of Representatives  Legislative Endor...