Dave Umahi ya ce gwamnatin tarayya ba zata iya ciyo bashi don biyan bukatun ASUU ba
Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi, ya ce gwamnatin Najeriya ba zata iya aro naira triliyan 1 don biya wa kungiyar malaman jami'oi ta ASUU da ta shafe watanni 5 cikin yajin aiki bukatun ta ba.
Shugaban kungiyar gwamnonin yankin kudu maso gabas din ya bayyana hakan ne ranar Laraba, a lokacin da ya karbi bakuncin wakilai daga sashin kudi na rundunar ‘yan sanda, a karkashin jagorancin Dakta Ben Akabueze a garin Abakaliki.
Kazalika ya yi Kira ga malaman jami'oin da Su taimaka Su sauko don a fahimci Juna, a kawo karshen yajin aikin.
Gwamnan har wayau ya koka Kan rashin habbaka al'adu, tare da bayyana bukatar gyara hakan a ko Ina a kasar nan.
Comments
Post a Comment