Gwamnan jihar Filato Simon Lalong a ranar Asabar ya ce ba zai taba cin amanar al’ummar jihar ba.
“A koyaushe zan ci gaba da kasancewa tare da jama’ar jihar domin ci gaban Filato.”
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron masu ruwa da tsaki da kungiyoyi daban-daban a Jos domin tattaunawa kan sake gina babbar kasuwar Jos.
Ya ce "Bari in bayyana karara cewa babbar kasuwar Jos za ta ci gaba da zama mallakin gwamnatin Jihar Filato da Hukumar Kasuwar Jos ke tafiyar da ita yayin da yarjejeniyar shekara 40 ta kasance ta daidaikun mutane da za su sayi shaguna ba bankin Jaiz ba."
Burina shi ne a gina kasuwa, in ji Lalong.
Gov Lalong ya kuma sha alwashin cika alkawuran yakin neman zabensa, a koda yaushe zan sanya maslahar jama’ar Filato a gaba a kowane lokaci, ina son al’ummar jihar nan da alheri kuma zan tsaya tare da su.
Ba na zo ne domin in lalata abubuwan gado ba, na kuduri aniyar inganta jihar.
Ya kara da cewa kasuwar Jos Terminus ce kaso 100 na jihar Filato.
Ina so al’ummar jihar su ci gaba da zaman lafiya da juna.
Comments
Post a Comment