Shugaban kungiyar malaman jami’oi ta kasa reshen jami’ar Yusuf Maimata Sule Dakta Surajo Sulaiman, yayi Allah ya wadai da kalaman karamin ministan kwadago, na cewa iyayen dalibai su roki kungiyar ASUU su koma bakin aikin su.
Dakta Surajo Sulaiman ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da Jaridar Dimokuraɗiyya, yau a Ofishinsa.
Ya kara da cewa kalaman ministan yana nuni da cewa gwamnatin tarayya ba da gaske take ba wajan biyawa kungiyar ta ASUU bukatun nata.
Yace, koda a makwannin da suka gabata sai da shugaban kasa Muhammad Buhari ya baiwa wani kwamiti daya kafa makwannin biyu, don warware matsalolin kungiyar.
Dakta Surajo Suleiman, ya kara da cewa makwanni 4, da kungiyar ta ASUU ta baiwa gwamnatin tarayyya yana nan bata janyen shi ba, kuma sunyi hakan ne dan yiwa ko wane bangare adalchi kafin daukar mataki na gaba.
Comments
Post a Comment