Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken da ke ziyara a Afirka ta Kudu, ya ce Amurka na zawarcin hulda ta gaskiya da nahiyar Afirka, sannan kuma ba ta gasa da wata babbar kasa a duniya wajen neman karbuwa a nahiyar ta Afirka.
Tun a Lahadin da ta gabata ce, Mista Blinken ya isa Afrika ta Kudu domin fara ran-gadin kasashen Afirka uku, wanda ke zuwa jim kadan bayan kammala ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Rasha, Sergei Lavrov ya kai nahiyar.
Shugaban Kasar Amurka Joe Biden |
A yayin gabatar da jawabi a taron manema labarai a babban birnin Pretoria na kasar Afrika ta Kudu, Sakataren Harkokin Wajen na Amurka ya ce, ba sa kallon nahiyar Afirka a matsayin wani fagen gogayya da manyan kasashen duniya.
A wannan ran-gadin da ya soma a nahiyar Afirka, Mista Blinken ya fara yada zango ne a Afirka ta Kudu, kasar da ke zama jagora a jerin kasashen duniya masu tasowa, wadda kuma ta dauki matsayin ’yan ba-ruwanmu a rikicin Rasha da Ukraine.
Mista Blinken din ya kuma sanar da wasu sabbin manufofin Amurka a nahiyar Afirka a wani jawabi da ya yi a jami’ar Pretoria.
Comments
Post a Comment