BELLO MUHAMMAD SHARADA YA RUBUTA
SHUGABANCIN MAJALISAR DATTIJAI
Ranar Talata mai zuwa wato 19 ga watan Yuli 2022, majalisar dattijai za ta koma bakin aiki. An yi hutun sallah. Zuwa ranar Lahadi 17 ga watan Yuli, duk wanda sunansa bai shiga cikin rumbum bayanai na masu takara ta shugaban kasa da mataimakansu da 'yan takara na majalisar dattijai da tarayya da INEC ta bude ba, an wuce gurin sai kuma in Allah ya kaimu kakar fidda 'yan takara na shekarar 2027.
'Yan majalisar dattijai masu ci guda 22 ne suka rasa takara, akasarinsu sun fito daga jam'iyyar APC. Wasu sun rasa kujerun ne sakamakon tafiya wata takarar, kamar shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, wanda yake neman shugabanci na kasa da abokinsa Sanata Abdullahi Adamu ya kwadaita masa, wasu kuma saboda sun canza takarar kamar Sanata Sabo Nakudu ya je neman gwamna a Jigawa, wasu kuma saboda rikicin su da gwamnoni na jihohin su kamar Kano da Kebbi da Jigawa. Sabuwar majalisar dattijai da za a yi ta 10 in tsaffin gwamnoni suka kai labari a jihohin su a ZABUKAN 2023, za a samu tsaffin gwamnoni 28 a majalisar, yawansu ya karu daga mutum 14, sun ninka sau biyu.
Ganin an samu faduwar zabe a Primary Elections, da shugaban jam'iyya na APC na kasa Sanata Abdullah Adamu da Sanata Kashim Shettima wanda yanzu shi ne dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar APC, Cif Bola Ahmed Tinubu, sun gana da shugaban kasa Muhammad Buhari gab da zai yi balaguro zuwa kasar Portugal a makon jiya, an yi zama domin warware matsalolin cikin gida na APC a majalisar dattijai amma, an tashi babu sakamako mai dadi da gamsarwa.
Daga ranar Talata zuwa Laraba da Alhamis bisa zance sahihi, wasu da yawa cikin sanatoci zasu fice daga jam'iyyar APC su koma wasu jam'iyyu. A halin da ake ciki akwai sanatoci 61 na jam'iyyar APC da kuma 48 na sauran jam'iyyun da suka hada da PDP da NNPP da APGA da Labor Party da YPP. Idan sanatoci 13 suka fice daga jam'iyyar APC, Ahmad Lawan shugaban majalisar dattijai shi kuma alkiyamarsa ta siyasa ta tashi. Zai rasa shugabancin majalisar dattijai kuma zai iya rasa kujerarsa ta takara wacce a yanzu ma ba shi INEC ta karba ba, dama kuma ya zo na hudu ne a takarar shugabancin Najeriya na APC. Uku babu kenan. Haka siyasa take, in kaine yau, gobe ba kai bane, wani ne. Wannan lissafin ya tabbata ba a samu canji, tunda harkar siyasa kamar sauyawar hawainiya yake.
In an samu wannan canjin mutum na farko da zai kwashi garabasa shi ne dan takarar shugabancin Najeriya na PDP Atiku Abubakar, mutum na biyu kuma da zai sharbi romo idan hakan ta kasance shi ne dan takarar shugabancin Najeriya a NNPP Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso. Wanda yake fuskantar babbar barazana kuma shi ne Bola Ahmed Adekunle Tinubu.
Shekarar zabe ta 2023 ta daban ce.
Comments
Post a Comment