: El-Rufai ya ce Buhari Bai Ma San Yan Ta'adda Sun Yi Barazanar Sace Shi Ba, Sai Da ya Sanar Da Shi
Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya ce shine ya fada wa Shugaba Muhammadu Buhari cewa yan ta'adda sun yi barazanar za su sace shi, rahoton Daily Trust. ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari.
A wani faifan bidiyo da aka saki a karshen mako, yan ta'ddan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a watan Maris, sun yi barazanar za su sace Buhari da El-Rufai.
Da ya ke magana a wani shirin rediyo da wakilin Daily Trust ya bibiya a daren ranar Lahadi, gwamnan yace shi kansa an masa gargadi ya rika takatsantsan da iyalansa.
Ya yi bayanin cewa, tun shekaru biyar da suka shude ya rika bada shawarar a yi wa yan ta'addan ruwan bama-bamai a duk inda suke, yana mai cewa wannan ne kawai mafita.
Gwamnan na Kaduna ya ce sojojin su bi yan ta'addan duk inda suke su gama da su.
Ya ce gaskiya sun damu da matsalar tsaro kuma suna fata gwamnatin tarayya za ta dauki matakin da ya dace.
Comments
Post a Comment