A yau Alhamis 21 ga watan Yuli, 2022, hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i da kwalejoji ta JAMB tare da shugabannin manyan makarantun kasar nan sun cin ma matsaya a kan mafi karancin sakamakon UTME don ci gaba da karatu a 2022/2023.
A cewar masu ruwa da tsakin, mafi karancin sakamakon UTME da ake bukata don shiga jami’o’i shi ne 140.
Haka nan, sakamakon da ake buƙata don shiga kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi, a tsayar da shi a kan maki 100.
Wannan hukunci an yanke shi a taron da ake cigaba da gudanarwa don samun matsaya a kan cigaban karatun ɗaliban wanda ministan ilimi, Adamu Adamu ya jagoranta a Abuja, Alhamis.
Comments
Post a Comment