Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami ne ya bayyana hakan yau bayan kammala zaman majalisar zartarwa ta ƙasa.
Ministan ya ce gwamnatin ta lura cewar ana amfani da babura wajen aikata laifuka daban-daban a don haka su ke duba yuwuwar haramta achaɓa a wani salo na kawo karshen ta’addanci.
A wani bincike da gwamnatin ta gano cewar ana amfani da babura wajen aikata laifi,haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da sauran ayyukan ta’addanci.
A wani zama da shugaban ya yi da ministan harkokin ƴan sanda da ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola.
Comments
Post a Comment