Mubarak Sani
Wani mai kula da ci gaban kadarorin. Aliyu Abubakar ya shaidawa wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja cewa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta nemi yayiwa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Mohammed Bello Adoke, tsohon lauyan gwamnatin tarayya kazafin laifin karkatar da kudade.
Da yake magana a gaban kuliya a ranar Talata a shari’ar da ake yi, Abubakar ya ce Bala Sanga, mai shigar da kara na EFCC a lokacin, ya tambaye shi ranar 31 ga Disambar 2019 cewa ya ba Adoke dala miliyan 2 da Jonathan dala miliyan 50 “domin kar naci gaba da zama a tsare har cikin sabuwar shekara”.
Ya ce daga nan ne aka tilasta masa sanya hannu a cikin takardar da aka shirya tare da barazanar cewa za a tsare shi ne bisa umarnin Ibrahim Magu, wanda shi ne Shugaban Hukumar EFCC a lokacin, idan bai ba hukumar hadin kai ba. The Cable ta ruwaito
Comments
Post a Comment