Dan Takarar shugabancin kasar nan na PDP a zaben 2023 Atiku Abubakar ya karbi bakuncin Jakadan Afrika ta Kudu a Najeriya Thamsanga Dennis Mseleku a gidan sa dake Asokoro.
Tattaunawar tasu a yayin zaman ta mayar da hankali ne kan yadda za a fadada dangantakar difulomasiyya tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu domin ya zama sanadiyyar karfafa dangantaka tsakanin kasashen Afrika da nufin Samar da tsarin da ake Bukata na Gina hadin Kai da tattalin arziki a Nahiyar.
Dennis Mseleku yace Najeriya na bukatar Mika Mulki cikin ruwan sanyi, inda ya yi alkawarin goyon baya Daga kasar sa domin Najeriya ta samu gudanar da ingantaccen zabe a 2023. Ya yabawa kasashen biyu bisa yunkurin su na sake karfafa alaka, yana Mai cewa abinda kasashen biyu suka fi Bukata a yanzu shi ne aiki a zahiri domin inganta tattalin arziki.
Comments
Post a Comment