Babbar Kotun Tarayyar Najeriya da ke zamanta a Abuja a yau Talata ta yanke wa wasu mutum biyu hukuncin zaman gidan yari na shekara shida.
Mutanen wato Chibunna Patrick Umeibe da kuma Emeka Alphonsus Ezenwane waɗanda ake yi wa shari'a tare da DCP Abba Kyari, an kama su ne da laifuka uku daga cikin laifukan da hukumar NDLEA da ke yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi ta shigar game da su.
An kama mutanen biyu ne a filin jirgin sama na Enugu a yayin da suke ƙoƙarin fasa ƙwabrin hodar ibilis.
Comments
Post a Comment