Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya, INEC, ta ce ba za ta sake kai kayan zaɓe masu muhimmanci ajiya ba a Babban Bankin Najeriya (CBN).
Da yake magana yayin wani taron ƙara wa juna sani a Abuja ranar Asabar, shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya ce daga yanzu CBN ba zai sake ajiye kayan zaɓen ba tun daga kan zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da za a yi ranar 18 ga watan Yuni.
Bisa al'ada, INEC kan kai kayan zaɓe kamar takardun jefa ƙuri'a da takardun rubuta sakamako da abin jefa ƙuri'a na masu lalurar ido ajiya a CBN kafin fara kaɗa ƙuri'ar yayin zaɓuka a Najeriya.
Sai dai babu tabbas ko matakin na da alaƙa da ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan rahotannin da ke cewa Gwamnan CBN Godwin Emefiele na son ya nemi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar - kodayake ya musanta batun.
Ya ce: "Muna duba yadda za mu inganta gudanar da ayyukan, saboda haka ba lallai ne hakan yana da alaƙa da abin da ke faruwa a CBN ba. Manufarmu ita ce a kodayaushe mu inganta da kuma gudanar da ayyukanmu da kanmu.
"Ba za mu yi amfani da CBN ba a zaɓen Ekiti, za a kai kayan zaɓen daga ofishinmu na Abuja zuwa filin jirgi sannan a kai su ofishinmu na jiha."
All is now set for the All Progressives Congress (APC) Presidential primary in Abuja holding from Monday, June 6 to June 7 at the Eagle’s Square with six aspirants in the lead, Jasawa Times learned. The presidentail aspirant include the Vice-President Yemi Osibanjo; former Minister of Science and Technology, Ogbonnaya Onu, Ebonyi Gov. Dave Umahi; former Lagos Gov. Bola Ahmed Tinubu, former Minister of Transportation, Rotimi Amaechi and ex-Minister of State for Education, Chief Chukwuemeka Nwajiuba. The Eagles Square is expected to host about 2,240 delegates from the 36 states and the Federal Capital Territory. Expectedly, the influx of people into the FCT has increased, a development that has attracted more police presence at the Eagles Square and some hotels hosting the delegates and chieftains of the APC. Ahead of the event, the party’s National Chairman, Sen.Abdullahi Adamu on Sunday visited the Eagles Square where he expressed satisfaction with the facilities put in place by...
Comments
Post a Comment