Daga 'Ya'yanta; Shawara Ta ZUWA GA GWAMNATI DA HUKUMOMI MASU RUWA DA TSAKI A BANGAREN AIKIN ASIBITI.
Daga Nasir Yusuf Jibril, Yola
Kamar yadda muka sani, majalisar ma'aikata masu kula da majinyata ta duniya (International Council Of Nurses) ta ayyana, ranar shida zuwa sha biyu ga watan mayu (6-12 May) na kowace shekara a matsayin ranar ma'aikata masu kula da majinyata (International Nurses Day), zan yi amfani da wannan dama inyi tsokaci da kuma ƙara jawo hankalin hukumomi da gwamnati kan irin hali da dabi'u da ma'aikata masu kula da majinyata da sauran ma'aikatan asibiti ke nunawa na rashin kwarewa da rashin sanin makaman aiki (Law and Ethics) akan mu'amalar su da majinyata da kuma masu jiran majinyata, musamman a jihar Adamawa, inda korafe-korafe yayi yawa kan yadda ma'aikatan asibiti ke nuna mummunar mu'amala na rashin ganin darajar mutane yayin aiki.
Ina amfani da wannan dama wajen jawo hankalin Majalisar ma'aikatan kula da jinya da ungozoma(Nursing and Midwives Council Of Nigeria), da kuma kungiyar gamayyar ma'aikatan kiwon lafya wato (Joint Health Sector Union), gwamnati, da sauran kungiyoyi masu ruwa da tsaki a bangaren kiwon lafiya.
Da farko dai, sanin kanmu ne cewa kowani fage na aiki na da ka'idoji da dabi'u na yin sa, wato (Law and Ethics). Ita ma wannan fage naku ba a barta kara zube ba, tana da nata dokoki da ka'idojin aiki.
Koke-koke sun yi yawa akan ma'aikatan asibiti musamman ma “nurses" da “midwives", wajen nuna mummunar mu'amala tsakanin su da majinyata da kuma masu jiran mai jinya.
Kusan yanxu idan ka kira sunan “nurse” a cikin mutane, babban ma'anar da zai fara zuwa ransu shi ne; rashin kunya, mummunar mu'amala, girman kai da sauran dabi'u na walakanci.
A nawa mahangar wannan mummunar mu'amala da ma'aikatan asibiti ke nunawa, tabbaci ne na rashin kwarewa da rashin sanin makaman aiki, sannan kuma tabbaci ne na rashin ma faɗi ko in ce sakacin masu faɗa aji ne a wannan fage, inda hakan ya janyo zubewar mutuncin ma'aikatan asibiti a idon mutane da dama, ya Kum sa a maimakon mu dinga ganin su a matsayin masu tausayi da ceto rayuwar al'umma, mun koma ganin su a matsayin masu nuna rashin tausayi da hallaka al'umma.
A makon Jiya, saura kadan na sharara wa wata “nurse" mari a sakamakon nuna rashin ɗa'a da ganin darajar dan Adam. Ba komai ya jawo haka ba sai rashin bin ka'idoji da kuma dokokin aiki (Law and Ethics) wanda ya janyo wa aikin baƙin jini da kuma mummunar fassara.
Bugu da kari, akwai wani ƙalubale ko in ce matsalar da take kara tinkaro fannin kiwon lafiyar mu, musamman mu nan Adamawa.
Wannan matsalar kuwa ita ce; fara yawaitar Makarantantu koyon harkar lafiya masu zaman kansu wanda ba a tantance su ba a hukuman ce ko in ce ba a gama tantance su ba a hukuman ce (un-acreditate private colleges of health...)
Yawan cin wayan nan makarantun din dalibai marasa kwarewa (quacks) kawai ake fitar wa...!
Domin galibin daliban Korarrun daliban kolejin horar da ma'aikatan jinya ta jihar Adamawa ne(nursing school, Yola.) ko makarantar koyon aikin lafiya( school of health) da ke mubi, suke dawowa nan.
Wanda a bayya ne ya ke an san wa 'yan can makarantun sun ginu ne kawai domin kasuwanci ba don inganta bangaren kiwon lafiya ba.
Don haka zaka tarar basa iya daukan kwararru wanda suka dade kuma suka samu gogewa a fan nin, domin baza su iya cire kudi su biya su yadda ya kamata ba, sai dai su dauko 'yan bana bakwai wanda kudi kadan zasu musu aiki.
Wannan dalili yasa cin hanci da alfarma ya shigo cikin harkar, inda ya kara nuna rashin kwarewan irin wa yan nan daliban a waje koyon san makaman aiki ( I.T) har ma bayan kammalawar su
Don haka laifin irin wayan nan daliban shi ke shafan kwararrun...!
jama'a kuma suke yin musu kudin goro...
A takaice dai abunda nake son fadi a nan shi ne; Makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu da ( Private schools of health) da su ke ta fitowa a Adamawa gaskiya ba alkhairi ba ne ga fanin kiwon lafiyar jihar, hasali sai dai a ce barazana ne ga fan nin.
Shawara ta zuwa ga kungiyoyi da hukumomi masu ruwa da tsaki kan harkar kiwon lafiya shi ne; Dalibai da ake yayewa musamman 'yan kolejin horar da ma'aikatan jinya (college of nursing) don matsalar tafi yawa daga wajen su, Ya kamata a saka musu darussan koyon sanin ka'idoji da dokokin aiki (Law and Ethics) tun daga ajin farko har zuwa ajin karshe, sannan kuma a musu jarabawa ta musamman akai.
Gwamnati da hukumomin kiwon lafiya su yalwata ofisoshin karban korafe-korafe na majinyata da masu jiran su, kan mu'amalar su da ma'aikatan asibiti. Kungiyoyi na kiwon lafiya musamman kungiyar “nursing and midwives” da sauran kungiyoyi masu ruwa da tsaki a bangaren kiwon lafiya, su dinga haɗa taron wayarwa al'umma kai game da ƴancin su da hakkokin su a kan ma'aikatan asibiti da ma asibiti baki ɗaya (na gwamnati da masu zaman kansu) musamman a irin wannan lokaci na bikin murnar satin ma'aikatan jinya wato (Nurses week).
Majalisar ma'aikatan jinya da ungozoma, wato (Nursing and Midwifery Council of Nigeria) ta dinga daukan mataki da ya dace a duk lokacin da ta samu rahoton taka dokokin aiki komai ƙanƙantar sa.
Yakamata hukumomi masu ruwa da tsaki da gwamnati su dai na bada lasisi ga makarantun da basu dace ba, idan ya kama dole toh sai a tabbatar da inganci su, kuma a sa musu ido kan dokokin da aka saka musu. Son samu ya zamanto gwamnati ne kawai ke da alhakin kafa makarantun kiwon lafiya.
Ina ga zai fi musu saukin kula, saɓanin idan sunyi yawa...!!!
Hausawa sun ce da haihuwar goma marasa amfani gara haihuwar daya mai amfani.
Kamar yadda gwamnati, ita kadai ke kula da harkokin da ya shafi tsaro da jami'an tsaro, ba tare da ta bawa wata ko wani mai zaman kan shi damar mallakar police ko soja ba, domin muhimmancin bangaren, haka muke fata suyi dokan hana mallakar makarantun kiwon lafiya ga Mutane ko in ce 'yan kasuwa masu zaman kansu, musamman a jihar mu da kasa ma baki daya, don samun daman baiwa bangaren kulawa yadda ya kamata.
Idan har aka karfafa waɗannan dokokin, to za'a samu daidaito akan wannan matsalar da muke fama da ita, don kowa zai tsaya a iyakarsa .
Allah ya kara rufa man asiri. Allah ya bai wa ma'aikatan lafiyar mu juriya, basira, da kuma jajircewa kan aikinsu. Marasa lafiyar mu, Allah ya basu lfya.
Wassalam.
Nasir Yusuf Jibril, Yola.
Daga jami'ar Bayero, Kano, Tsangayar sadarwa, sashen koyon makaman aikin jarida.
Comments
Post a Comment