Skip to main content

JAMUS TA WARE EURO BILIYAN 65 DOMIN RAGE WA JAMA’A RADADIN RAYUWA

 



Gwamnatin Jamus ta ware Euro biliyan 65 domin rage wa iyalai da kamfanoni radadin tsadar makamashi da suke fuskanta a halin yanzu.

Gwamnatin ta ce ta kaddamar da sabon shirin don taimaka wa magidanta shawo kan hauhawar farashin kayayyaki ne.

Haka kuma, ta ce tana sa ido kan ribar da kamfanonin makamashi ke samu don taimakawa wajen samar da tallafin.

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, ya ce sun dauki matakan gaggawan ne saboda lokacin sanyin hunturu da ke gabatowa don saukaka wa al’umma samun saukin dumama gidajensu.

Sanarwar wannan mataki  ta zo ne bayan matakin da Rasha ta dauka na katse samar da makamashin iskar gas ta bututun “Nord Stream 1" wanda ke samar wa kasashen Turai makamashin.

Jasawa times ta ruwaito cewa, Tsarin rage radadin karo na uku, zai hada da rage wa mutane kudin tikitin tafiye-tafiye da na wuta da iskar gas ga ’yan fansho da dalibai da ma sassauta wa kamfanoni da ke cin makamashi sosai.

Yanzu haka ’yan kasuwa da masu saye a Jamus na jin radadin tsadar makamashi da ya yi mummunan tashi, yayin da kasar mafi girman tattalin arziki a Turai ke neman hanyoyin janye kanta daga dogaro da kayayyakin Rasha a  sakamakon mamayar da ta yi wa Ukraine.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu yanzu: 'yan majalisar dattijai sun tafi hutu domin gudanar da yaƙin neman zaɓe

Majalisar dattijan Nigeria, sun tafi hutu a yau Laraba, domin samun cigaba da gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓe a jam'iyyun da suke ciki, don tunkarar babban zaɓen shekarar 2023, kamar yadda shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan, ya bayyana yayin zaman majalisar na wannan rana. Lawan yace zace zasu tafi hutun ne domin tabbatar da abubuwa sun zama cikin tsari a ƙasar nan, kuma za su dawo a ranar 28 ga watan Fabrairu, kwanaki uku kenan bayan an gudanar da zaɓen shugaban ƙasa dana yan majalisun tarayya, kafin su sake tafiya wani hutun a ranar 1 ga watan Maris, domin gudanar da zaɓen gwamnoni da yan majalisun dokokin jiha, da za'ayi a ranar 11 ga watan Maris. Cikin jawabinsa, Lawan yayi kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, da kuma jami'an tsaro, akan su tabbatar sunyi ayyukansu yadda ya dace, domin yin zaɓe cikin kwanciyar hankali da lumana, karbabben zaɓe kuma sahihi. Majalisar Nigeriya

Bridging Digital Divides: Empowering People with Special Needs and Uniting Communities Through Technology

By Abdullahi Abdulhafiz Aliyu In today’s fast-changing digital landscape, access to technology is no longer a luxury—it is a necessity. Yet, for millions of Nigerians, especially people with special needs, the digital world remains out of reach due to systemic barriers and a lack of inclusive learning opportunities. My work as a journalist and digital advocate has focused on breaking these barriers, ensuring that technology serves as a tool for empowerment rather than exclusion. Through my engagement with individuals with disabilities and as the host of Duniyar Fasaha (Fasaha World) on Unity FM, I have worked to bridge the digital divide by providing foundational digital education to marginalized groups. By introducing people with special needs to basic computer skills such as Microsoft Word, Excel, PowerPoint, and internet navigation, I have witnessed firsthand how technology can unlock new opportunities and transform lives. Digital Skills for Special Needs: A Path to Inclusion Inclu...

All Is Set For APC Presidential Primary.

All is now set for the All Progressives Congress (APC) Presidential primary in Abuja holding from Monday, June 6 to June 7 at the Eagle’s Square with six aspirants in the lead, Jasawa Times learned. The presidentail aspirant include the Vice-President Yemi Osibanjo; former Minister of Science and Technology, Ogbonnaya Onu, Ebonyi Gov. Dave Umahi; former Lagos Gov. Bola Ahmed Tinubu, former Minister of Transportation, Rotimi Amaechi and ex-Minister of State for Education, Chief Chukwuemeka Nwajiuba. The Eagles Square is expected to host about 2,240 delegates from the 36 states and the Federal Capital Territory. Expectedly, the influx of people into the FCT has increased, a development that has attracted more police presence at the Eagles Square and some hotels hosting the delegates and chieftains of the APC. Ahead of the event, the party’s National Chairman, Sen.Abdullahi Adamu on Sunday visited the Eagles Square where he expressed satisfaction with the facilities put in place by...