Kwamitin haɗin gwiwa na ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU) da na ƙungiyoyin ma’aikata sashen da ba koyarwa ba (NASU) sun dakatar da yajin aikin da suke yi na tsawon watanni biyu.
Wani mamba a kungiyar haɗin gwiwar kuma shugaban SSANU na ƙasa, Mohammed Ibrahim ne ya bayyana hakan a wata hira da jaridar The Nation ta wayar tarho ranar Asabar a Abuja.
Ya ce dakatarwar za ta fara aiki ne daga ranar Larabar mako mai zuwa. “Eh, mun dakatar da yajin aikin na tsawon watanni biyu,” in ji shugaban SSANU.
A cewar Ibrahim, gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 50 domin biyan alawus-alawus ga mambobin SSANU, NASU da kuma ƙungiyar malaman jami’o’i ta ASUU.
Ya kuma ce ƙungiyoyin sun cim ma yarjejeniya da gwamnati kan sharuɗɗan dawowa bakin aikinsu da fatan za a aiwatar da yarjejeniyar cikin watanni biyu.
Yajin aikin da SSANU da NASU suka yi, ya sa aka dakatar da bayar da takardun shedar kammala karatu, da kuma gudanar al’amuran sa suka shafi tafiya aikin hidimar ƙasa na NYSC.
A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, shugaban SSANU ya ce: “A yau, bayan tattaunawa da mai girma ministan ilimi da kuma gamsuwar da muka cewa gwamnati a wannan karon za ta jajirce wajen amincewa da mutunta yarjejeniyoyin da aka cim ma a tarurrukan da aka yi, muna sanar da ku wata tazarar watanni biyu da muka bai wa gwamnati don aiwatar da yarjejeniyar da aka cim ma.
“Burinmu ne, ganin irin tabbacin da mai girma ministan ilimi ya yi da kuma jajircewarmu na ganin an kawo karshen rikicin da ke faruwa, cewa damar da za a samu na watanni biyu zai isa a ɗauki matakan da za su kawo ƙarshen saɓanin gaba daya”
Comments
Post a Comment