An yi kira ga iyaye su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin da Allah Ya daura mu su na tarbiyantar da ‘ya‘yayen su yadda ya kamata.
Kazalika an shawarce su da su rika mayar da hankali akan harkokin yaran na yau da kullum don gujewa jefa su halin ni ‘ya su.
Mai Unguwar Rogo/Layin Dan Badawai dake nan birnin Jos din jihar Pilato, Alhaji Aliyu Muhammad Dan Badawai ne yayi wannan Kira ranar Asabar, a wajen taron yaye dalibai na shekara-shekara da Makarantar Skyline ta shirya a nan cikin garin Jos.
Mai Unguwa Dan Badawai daya kasance bako mai jawabi a wajen taron, ya tunatar da al'umma cewa, Allah Ya halicce su ne don su bautata Mishi, yana mai cewa, ta hanyar neman ilimi ne mutum zai san hanyoyin dazai bi wajen bautatawa.
A lokacin da yake Jan hankalin iyaye da suke nuna halin ko inkula akan karatun ‘ya‘yan Su, Alhaji Aliyu Dan Badawai ya shawarcesu dasu tuna da yadda haduwar Su da Ubangiji zata kasance, domin kuwa a cewar Shi, za'a tambayi kowa akan kiwon da aka bashi.
Game da halin tsadar rayuwa da ake ciki kuwa, Alhaji Danbadawai ya shawarci al'umma suyi hakuri da wannan jarabawa don samun dacewar Ubangiji.
A nashi tsokacin mu'assashin Skyline, Malam Ahmad Abubakar Ahmad, ya bukaci iyaye da su cigaba da bayar da hadin Kai wajen ilimantar musu da Yara, ya na mai Mika godiyar shi wa mahalarts taron abisa amsa gayyatar da ka yi mu Su.
Jasawa times ta rawaito cewa, kansilan Anguwan Rogo/Rimi/ Sabon Layi, wato Honourable Sulaiman Sultan ta bakin Wakilan Shi, ya jaddada muhimmancin baiwa Yara tarbiya don kaucewa jefasu kan mummunar hanya.
Comments
Post a Comment