Daga Mubarak Sani
Gwamnatin Jihar Plateau ta haramtawa kungiyar Kwadago zanga-zangar gama gari da take shirin yi gobe Talata a fadin kasar.
Sanarwar da ta fito daga fadar Gwamnatin jihar a yammacin yau litinin 25, ga watan Yulin 2022 ta bayyana cewa Gwamnatin jihar ta samu labarin shirin zanga-zangar inda tace baza ta amince da ita ba.
Gwamnatin ta bayyana cewa tana sane da dokar da ta bawa ma'aikata damar gudanar da zanga-zanga amma saidai har yanzu Jihar bata gama murmurewa ba daga tashe tashen hankula. Bugu da kari dama akwai dokar da aka sanya a baya wacce ta haramta duk wata irin zanga-zanga a fadin jihar kuma har yanzu ta nan.
Sanarwar ta kara da cewa kungiyar tayi gaggawar janye zanga-zangar domin baza a bari wasu bata gari suyi angulu da kan zabo ba domin bata zaman lafiyar da aka samu.
Daga karshe, Gwamnatin tace ta baza jami'an tsaro lungu da sako na fadin jihar domin tabbatar da doka da oda tare da hukunta duk wanda aka gani da sunan zanga-zanga.
Idan ba a manta ba dai, kungiyar Kwadagon ta NLC a makon daya gabata ta fitar da sanarwar gayyata ga rassanta na fadin kasar domin goyawa kungiyar malaman jami'a baya saboda kawo karshen yajin aikin da aka kwashe sama da watanni biyar anayi.
Comments
Post a Comment